Ana iya tsige gwamna Ganduje daga kujerarsa matuƙar bai naɗa babban Alkalin jihar Kano ba

Ana iya tsige gwamna Ganduje daga kujerarsa matuƙar bai naɗa babban Alkalin jihar Kano ba

- Barista Audu Bulama Bukarti yayi kira ga majalisar dokokin jihar Kano ta tsige Ganduje

- Bulama ya bukaci gwamnan ya gaggauta nada babban alkalin jihar Kano.

Fitaccen dan gwagarmaya, kuma dank are hakkin bil adama, Barista Audu Bulama Bukarti ya aika ma majalisar dokokin jihar Kano wasika, inda ya bukaci gwamnan ya gaggauta nada babban alkalin jihar Kano.

Cikin wasikar da Bukarti ya aika ma majalisa, ya bukaci dasu tilasta ma gwamna Ganduje ya nada babban jojin jihar Kano kamar yadda, Leadershio Hausa ta ruwwaito, ko kuma su tsige shi, idan yaki amsa bukatarsu.

KU KARANTA: Zaɓen 2019: Atiku sai ya nemi gafarar Obasanjo muddin yana son zama shugaban kasa a Najeriya

Bulama yace rashin nada babban alkalin jihar ya saba ma sashi na 271 (5), (1) na kundin tsarin mulkin kasa. Bugu da kari Lauyan yayi barazanar daukan mataki idan majalisar bata dauki mataki ba cikin sati daya.

Ana iya tsige gwamna Ganduje daga kujerarsa matuƙar bai naɗa babban Alkalin jihar Kano ba

Bulama

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Bukarti yana karin bayani kamar haka:

“Mun ja hankalin majalisa cikin waiskar da muka aikata mata dangane da karar tsaye da Gwamna yayi ma kundin tsarin mulki kan batun nada babban jojin jijar Kano, idan kuma yaki, suna iya tsige shi duba da sahi na 88 na kundin tsarin mulki.” Inji Bulama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel