Bayafara: Gwamnatin Tarayya ce musabbabin rarrabuwan kai a Najeriya - Sa'ad Abubakar II

Bayafara: Gwamnatin Tarayya ce musabbabin rarrabuwan kai a Najeriya - Sa'ad Abubakar II

- Sarkin ya ce rashin adalci da nuna bamabamci tsakanin al'umma shi ne silan rarrabuwan kai a Najeriya

- Ya fadi hakan ne ta bakin wakilin sa a wani taro da a ka yi a Abuja

- Sarkin ya yi kira ga shuwagabanni da su kasance masu adalici a tsakanin al'umma

Sa'ad Abubakar II, Sarkin Musulmi, kuma Shugaban Kungiyar Koli na Harhakokin Musulunci, ya ce rashin adalci wurin rarraba mukamai da kuma nuna fifiko wurin aikace-aikace shi ne musabbabin rarrabuwan kai a Najeriya.

Sarkin ya fadi haka ne ta bakin wakilin sa, Ibrahim Jega, a wani taro na zaman lafiya da a ka yi a Abuja, ranar Laraba. Abubakar ya ce gwamnati wacce ba ta nuna wariya ko fifiko ce ke iya magance matsalolin da Kasar ta ke fuskanta.

Bayafra: Gwamnati na da hannu wajen raba kawunan Najeriya, Inji Sarkin Musulmi

Bayafra: Gwamnati na da hannu wajen raba kawunan Najeriya, Inji Sarkin Musulmi

Sarkin musulmin ya yi kira ga shuwagabanni na ko wani mataki da su kasance masu adalci tsakanin mutane, ka da su nuna bamabamcin addini ko siyasa ko kabila.

KU KARANTA: Hukumar NNPC tayi alkawarin tallafawa kamfanonin Najeriya da ke harakar man fetur

A cewar sa, idan a na maganar sauke nauyin shugaba a kan jama'ar sa, to babu yadda kiyayya ko soyayya zai shigo ciki. Ana sauke nauyin ne bisa adalci.

Sarkin ya ce haka Allah ya umurce shugaba ya yi adalci, ka da ya bari kiyayyar sa ga wata al'umma ya hana shi yi masu adalcin. Kuma kada nuna bamabamci ko fifiko.

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel