Kabilar Igbo zai shugabanci Najeriya bayan Buhari ya kammala wa’adi na biyu – Inji Kalu

Kabilar Igbo zai shugabanci Najeriya bayan Buhari ya kammala wa’adi na biyu – Inji Kalu

- Kalu ya ce Igbo ne zai shugabanci Najeriya bayan shugaba Buhari ya kammala wa’adi na biyu

- Tsohon gwamnan jihar Abiya ya kwantar wa Ndigbo hankali a kan shugabancin Najeriya

- Tsohon gwamnan ya ce makomar Igbo a siyasar Najeriya ya fi haske yanzu a jam’iyya mai mulki, APC

Tsohon gwamnan jihar Abiya kuma babban jigo a jam’iyya mai mulki ta APC a jihar, Cif Orji Kalu, ya ce ‘yan kabilar Igbo su kwantar da hankalinsu, cewa idan sun zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu, shaka babu sune za su yi shugaban Najeriya a 2023.

Kalu, wanda ya bukaci Igbo don farkawa da kuma koyi daga abubuwan da suka gabata na siyasa, ya bayyana cewa "makomar Igbo a siyasar Najeriya ya fi haske a yanzu fiye da yadda ya kasance tare da APC".

Kalu, wanda ya yi jawabi a Umuahia, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba, ya ce samun shugabancin kasar alhaki ne wanda ya rataya a kan dukkanin ‘yan kabilar Igbo kuma yanzu haka jam’iyyar APC ne mafi dacewa da za su iya cimma wannan burin.

Igbo za ta yi shugabancin Najeriya bayan Buhari ya kammala wa’adi na biyu – Inji Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abiya, Cif Orji Kalu

Ya ce, "Makomar Ndigbo tana da haske a jam’iyyar APC. Da zarar shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa karo na biyu, ina tabbatar muku cewa ni da duk wani mutumin Igbo muna da damar samu shugaban Najeriya. Abinda ya kamata a yi yanzu shine mu marawa wannan gwamnati baya”.

KU KARANTA: Kungiyar matasan Najeriya sun kaddamar da goyon bayansu ga sake tsayawa takaran shugaba Buhari

"Ba’a mu buƙatar wani abu fiye da ofishin shugaban kasa. Idan kun ga abin da na yi a kauyuka a matsayin gwamna, za ku san irin ci gaban da za ku iya samu idan iri na ya zama shugaban kasa, kun san cewa Najeriya za ta ci gaba. Ndigbo za su ji dadin kasancewa a APC saboda nan gaba tana da haske jam’iyyar. Wannan shine dalilin da ya sa muke kokarin lashe zaben jihar Anambra kuma da yarda Allah za mu ci nasara a jihar”, inji shi.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, Kalu ya bayyana cewa gwamnatin APC a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta fara sake gina hanyar Uzuakoli zuwa Bende Ohafia a jihar wanda shine ya kai kuka ga shugaban kasa akan bukatar gyaran hanyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel