Abubuwan da Buhari zai yi domin samun kashi 75 na kuri'un Ibo a 2019 - Orji Kalu

Abubuwan da Buhari zai yi domin samun kashi 75 na kuri'un Ibo a 2019 - Orji Kalu

- Ya ce idan har Buhari ya ba yankin su Muhimmanci, za su ba shi kashi 75 na kuri'un su

- Ya ce yankin na su wutan lantarki da tituna kadai su ke bukata don sana'anta da duk wani abu da ake bukata

- Ya kuma soki wadanda su ka sayar da ma'aikatun wutan lantarki

Orji Uzor Kalu, tsohon Gwamnan Jihar Abia, ya ce Buhari zai iya samun kashi 75 na kuri'un mutanen Kudu maso Gabas a 2019 idan har ya iya magance matsalolin da su ke fuskanta. Ya yi wannan bayani ne a tattaunawar da ya yi da tashar labarai na Arise.

Abubuwan da Buhari zai yi domin samun kashi 75 na kuri'un Ibo a 2019 - Orji Kalu

Abubuwan da Buhari zai yi domin samun kashi 75 na kuri'un Ibo a 2019 - Orji Kalu

A ta bakin sa, ''Idan Shugaban Kasa ya yi niyyar sake tsayawa takara, zamu tursasa shi ne ya ba yankin mu muhimmanci, ta haka ne zamu ba shi kashi 75 na kuri'un mu. Wurare irin su Aba da Onitsha za su iya sana'anta duk wani abun bukata idan har a ka ba su wadataccen wutan lantarki.''

KU KARANTA: Dokar Hana Yawon Kiwo: A na zargin Fulani Makiyaya da kashe wani mutum

''Idan a ka bamu wuta da tituna masu kyau kadai, zamu iya sana'anta duk wani kayaki 'yan China a Aba da Onitsha, tuni a ke yin hakan a Nnewi. Hatta kayakim kimiyya da fasaha duk za mu iya yi idan har a ka bamu kwarin gwiwa.''

''Wadanda su ka sayar da ma'aikatun samar da wutan lantarki sun yi son rai. Don kuwa sun bayar da su ne ga abokanan su, wanda yin hakan ba daidai bane.'' In ji shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel