Hajiya Baraka Sani ta fito takara wani mukami a Jam’iyyar PDP
- ‘Yar siyasar Kano Baraka ta fito takara a Jam’iyyar PDP
- Baraka Sani na neman kujerar Shugaban mata na Kasa
- Ta ce dole mata su dage domin a rika tafiya da su a siyasa
Tsohuwar Kwamishinar Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso a lokacin yana mulki watau Hajiya Baraka Sani ta fito neman kujera a Jam’iyyar PDP.
Kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar aily Trust, Baraka tana neman mukamin na Shugaban mata na Kasa a Jam’iyyar PDP ne domin ta ingantawa mata a Kasar nan. Baraka Sani dai tayi aiki da Kwankwaso kafin ta sauya sheka.
KU KARANTA: Ministan sadarwar yace zai fito Gwamna a 2019
Baraka take cewa Jam’iyyar su ta PDP ita ce Jam’iyyar da za ta ba kowa dama ya kai matsayin da yake hari a kasar nan. Baraka dai ta shiga Gwamnati don haka tace ya kamata a rika tafiya da mata a Kasar a harkar siyasa a Najeriya.
Hajiya Baraka na kokarin ganin an samu kasha 35 na mukaman Gwamnati su zama hannun mata. Amma ‘Yar siyasar tace idan ba a tashi tsaye ba, ba za a ci ma wannan buri ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng