Sarki Sanusi ya kaddamar da Kamfanin Inshoran Musulunci na farko a Najeriya

Sarki Sanusi ya kaddamar da Kamfanin Inshoran Musulunci na farko a Najeriya

- Wannan kamfani shi ne irin sa na farko a Naneriya

- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kaddamar da ita jiya a Kano

- Ya ce Kamfanin na kowa da kowa ne ba na Musulmai kadai ba

A jiya Litini ne Sarkin Kano Muhammau Sanusi II ya kaddamar da Kamfanin Inshora a Kano. Kamfanin mai suna ‘Jaiz Takaful Insurance’, shi ne irin sa na farko a Najeriya.

Sanusi ya ce wannan irin cigaba abun farin ciki ne domin kuwa tsarin Kamfanin zai habaka tattalin arzikin Kasa.

Sarki Sanusi ya kaddamar da Kamfanin Inshoran Musulunci na farko a Najeriya

Sarki Sanusi ya kaddamar da Kamfanin Inshoran Musulunci na farko a Najeriya

Ya ce Kamfanin zai taimakawa kananan 'ya kasuwa wurin maye gurbin kayakin da su ka rasa ta hanyar wani wani bala'i da ka iya faruwa.

DUBA WANNAN: Sanatoci za su tattauna da Fashola game da farashin wutan lantarki

Ya kuma ce Kamfanin ba na Musulmai ne kadai ba, na kowa da kowa ne. Kamfanin zai tafiyu ne a kan tsarin shari'a don tabbatar da an tsayar da gaskiya da adalci ga kowa.

Sanusi kuma ya yi kira ga Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da ya yi wa kayakin gwamnatin Jihar, musamman gidaje da motoci, rajista da Kamfanin Inshora ta Jaiz Takaful.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel