Nigerian news All categories All tags
Takarar El-Rufai na 2019: Mutanen Kaduna ne zasuyi zabe ba shugaba Buhari ba

Takarar El-Rufai na 2019: Mutanen Kaduna ne zasuyi zabe ba shugaba Buhari ba

- Wani jigo a jam'iyyar APC a Kaduna, Tom Miayshi ya cacaki gwamna El-Rufai bayan ya bayyana niyyar sa fitowa takara zaben 2019

- Maiyashi yace kawai domin Buhari yana goyon bayan gwamna El-Rufai ba shine zai sa yaci zaben ba domin al'umma ne ke zabe ba shugab Buhari ba

Tsohon kwamishinan ilimi kuma jigo a jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Tom Maiyashi ya misalta goyon baya da Shugaba Buhari ya baiwa Gwamna Nasir El-Rufai na sake yin takara a zaben 2019 a matsayin abin dariya.

A cewar Maiyashi, duk wani goyon baya da shugaba Buhari zai baiwa El-Rufai baza tayi tasiri ba a jihar tunda al'ummar jihar ne zasuyi zaben.

Takarar El-Rufai na 2019: Mutanen Kaduna ne zasuyi zabe ba shugaba Buhari ba

Takarar El-Rufai na 2019: Mutanen Kaduna ne zasuyi zabe ba shugaba Buhari ba

A wata hira da yayi da jaridar Sun, jigon Jam'iyyar APC din yace koda tsani shugaba Buhari yayi amfani dashi wajen daga El-Rufai, ba zaiyi nasara sai dai idan al'umman jihar kaduna ne sukayi niyyar zaben sa kuma babu wanda zaiyi musu da wannan maganar.

KU KARANTA: Hukumar kwastam tayi nasarar cafke kwalaye 850 na miyagun kwayoyi

Maiyashi ya cigaba da cewa "Gwamna El-Rufai ya taba cewa dakikin dalibi ne kawai ke maimaita aji sau biyu, yanzu yana nufin shima ya zama dakikin ne shiyasa yake so ya maimata aji?

''Toh ya sani nine headimastan wannan ajin kuma zan daidaita masa zama, Ai ina tunanin mun koyar dashi da kyau amma tunda yace yana so ya maimata ajin, muna masa fatan alheri.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel