Yanzu-yanzu: Boko Haram ta kai hari a Yobe
- Har yanzu Boko Haram na nan na sheke ayar ta
- Sun kai hari a wani kauye a Yobe
- Ana nan ana bincike iyakacin barnar da suka yi
A ranar Talata wadansu 'yan Boko Haram suka kai mummunan hari a kauyen Sasawa, da ke karamar hukumar Damaturu, a jihar Yobe.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Abdulmalik Somunu, ne ya gaya wa manema labarai.
Yace har yanzu dai ana bincike a ga iyakar munin harin.
DUBA WANNAN: Kotu ta aike da shi gidan wakafi saboda ya jefe wata mata har lahira
An dade ba'a kai hari ba a yankin, saboda haka yawancin wadanda suka yi gudun hijira duk sun dawo ana ta noma.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:
labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng