Allah Sarki: Uwar yara 3 da ta kamu da kanjamau tace mutuwa ce kawai sauran gatanta

Allah Sarki: Uwar yara 3 da ta kamu da kanjamau tace mutuwa ce kawai sauran gatanta

- Mijinta ne ya sanya mata cutar ta kanjamau, kuma shi tuni ya mutu

- Matar tana da yara 3 kuma tana neman agaji daga jama'a

- Tace mutuwa ce kadai ta rage mata

Wata baiwar Allah mai suna Rakiya Zubairu ta zanta da jaridar Punch, inda ta ke nuna irin bakar wahala da take ciki bayan da mijinta ya saka mata kwayar cutar HIV ya kuma mutu ya barta da yara uku, wadanda aka sanya hotonsu a kasa.

Allah Sarki: Uwar yara 3 da ta kamu da kanjamau tace mutuwa ce kawai sauran gatanta
Allah Sarki: Uwar yara 3 da ta kamu da kanjamau tace mutuwa ce kawai sauran gatanta

A cewarta dai ba a son ta ubanta ya aurar da ita ba a shekaru 15 da haihuwa, kuma bata yi wani karatun kirki ba, tayi bautar aure har ta shekara 20. A yanzu shekararta 35 amma yaranta biyu da ita duk suna fama da cutar ta HIV.

Tace tun a 2008 ta kamu da cutar, kuma a lokacin likitoci sun gwada sunce batta da cutar, sai dai kwatam sai aka gano ashe tarin TB da take dashi kanjamau din ce ta kawo.

DUBA WANNAN: Mayakan Neja Delta sun sace Jamusawa 6 a ranar Asabar

Tace dai ko da mijinta ya aure ta a Kaduna yana da mata, amma sun rabu, sai dai koda ya gane yana da cutar a 2005, bai gaya mata ba, har sai da ya tabbatar itama ta kamu, sannan yanzu yaransu biyu suma sun kamu.

Ta ce dai saboda matsin rayuwa da talauci da yunwa, ga kuma cutar, babu taimako, takan yi fatan ta kashe kanta da yaran domin su huta da wahalar rayuwa. Ta ce koda yake magungunan kyauta ne, ko kudin zuwa asibiti takan rasa. Kuma akwai wasu magungunan da sai da kudi za'a bayar.

Da aka tambaye ta ko iyayenta sun sani, tace babanta yace ta manta da maganar, babu wani abu wai shi kanjamau a duniya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel