Makarantun da Gwamnonin Arewa su kayi karatun Digiri ko Difloma

Makarantun da Gwamnonin Arewa su kayi karatun Digiri ko Difloma

- Za ku ji Makarantar da kowane Gwamnan Arewa yayi

- Gwamnoni kusan 8 su kayi karatu a Jami’ar A.B.U Zaria

- A ciki akwai Gwamnonin da su kayi karartu a Kasar waje

Mun kawo jerin Makarantun da Gwamnonin Arewacin Najeriya su kayi karatu a lokacin su na kokarin neman ilmin Digiri ko babbar difloma kamar yadda mu ka samu.

Makarantun da Gwamnonin Arewa su kayi karatun Digiri ko Difloma
Wasu Gwamnonin Arewa a wani taro

Gwamnan Jihar ADAMAWA

Gwamna Bindo Jibrilla yayi karatu ne kan fannin kasuwanci a Birnin Landan a shekarun 1984 zuwa 1986.

Gwamnan Jihar BAUCHI

Shi kuma Barista Mohammed A. Bello yayi karatu ne a Jami’a Ahmadu Bello university (ABU) ta Zaria daga 1975 har 1978 a harkar sharia.

Gwamnan Jihar BENUE

Mista Ortom Samuel na Benue state yayi karatun sa ne a Ahmadu Bello ta Zaria a 1995 inda yayi Difloma yayin da ya koma Jami’ar gida yayi Digiri.

KU KARANTA: Farashin man fetur ya tashi a kasuwar Duniya

Gwamnan Jihar BORNO

Gwamna Kashim Shettima ya karanta harkar noma ne a Jami’ar Tarayya ta UNIMAID da ke Borno ya kuma kammala a shekarar 1989.

Gwamna Jihar GOMBE

Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na Gombe ya karanta harkar akanta ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria inda ya kammala a shekarar 1985.

Gwamnan Jihar JIGAWA

Gwamna Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa yayi karatu ne shi ma a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a wajen fannin akawu.

Gwamnan Jihar KADUNA

Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ya gama ne da sakamako mai kyau a bangaren gina-gine a Jami’ar nan ta Ahmadu Bello.

Gwamnan Jihar KANO

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano yayi karatun Digiri ne a Jami’ar Ahmadu Bello a Zaria daga shekarar 1972 zuwa 1975.

Gwamnan Jihar KEBBI

Alhaji Abubakar Atiku Bagudu yayi karatun Digiri ne a harkar tattali ne a Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto.

Gwamnan Jihar KOGI

Gwamna Yahaya Bello yayi karatun akawu ne a Jami’ar Ahmadu Bello na Zaria daga 1996 zuwa shekarar 1999.

Gwamnan Jihar KWARA

Gwamna Abdufatah Ahmed na Jihar kwara yayi karatun sa ne na Difloma da Digiri a gida Jihar Kwara daga shekarun 1978 zywa farkon 1980’s.

Gwamnan Jihar NASARAWA

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura yayi karatun sa ne a harkar koyar da karatu a babbar Jami’ar ta Ahmadu Bello a Zariya daga shekarar 1975 zuwa 1978.

Gwamnan Jihar Neja

Gwamna Abubakar Sani Bello yayi karatun sa ne daga 1986 zuwa 1991 a kan harkar tatalin arziki a Jami’ar Maiduguri.

Gwamnan Jihar Filato

Simon Bako Lalong na Jihar Filato yayi karatu ne a kan fannin shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello na Zaria a shekarar 1990.

Gwamnan Jihar SOKOTO

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto yayi karatun ilmin shari’a ne a Jami’ar Usmanu Danfodiyo a shekarar 1991.

Gwamnan Jihar TARABA

Shi ma Gwamna Darius Dickson Ishaku yayi karatu ne a Jami’ar Ahmadu inda yak ware a harkar gina-gine.

Gwamnan Jihar YOBE

Gwamna Ibrahim Geidam shi ma yayi karatun Difloma da Digiri ne a fannin akantanci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga farkon 1980’s zuwa 1990.

Gwamnan Jihar ZAMFARA

Shugaban Gwamnonin Kasar Abdulaziz Abubakar Yari yayi karatun satifiket ne da difloma a sha’anin sakatariya a shekarar 2004 a Garin Sokoto.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

.

Source: Legit

Online view pixel