EFCC ta ƙaddamar da sabuwar farautar Abdulrasheed Maina

EFCC ta ƙaddamar da sabuwar farautar Abdulrasheed Maina

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta sanar da sake kaddamar da farautar tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fanshi, Abdulrashid Maina, inji rahoton Premium Times.

A shekarar 2013 ne aka sallami Maina daga aikin gwamnatin tarayya, sakamakon kama shi da aka yi da badakalar satar kudaden yan fansho,inda duk kokarin da EFCC tayi na kama shi, hakan ya ci tura, daga nan kuma ya sulale ya bar kasar, inda a shekarar 2015 yan sandan Duniya suka fara nemsa wurjanjan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Turkiyya

Abin mamakin shine sai ga shi a wannan gwamnatin ta Buhari, mai karajin yaki da rashawa, an samu rahoton shigo da Maina Najeriya, kuma har an mayar masa da mukaminsa a ma’aikatar cikin gida, inda aka bashi darakta mai kula da ma’aikata.

EFCC ta ƙaddamar da sabuwar farautar Abdulrasheed Maina

Abdulrasheed Maina

Sai dai ministan ma’aikatar cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya wanke kansa daga wannan zargi,inda yace ofishin sakataren gwamnatin tarayya da na shugaban ma’aikatan gwamnati ne keda hakkin aiko da duk wani ma’aikaci mai mukamin darakra zuwa ma’aikatun da suka dace.

Haka zalilka, majiyar ta ruwaito an mayar da Maina ne bayan ministan shari’a Abubakar Malami ya bada shawarar yin hakan, musamman ta duba da dokokin kasa. Amma Kaakakinsa Salihu Othman ya musanta hakan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan rahoton mayar da Maina mukaminsa ne ya bata ma hukumar EFCC rai, inda ba tare da bata lokaci ba shugaban hukumar, Ibrahim Magu ya kira taron gaggawa don tsara yadda zasu kama shi.

Wani wanda ya halarci taron ya shaida ma majiyar mu cewar a yayin zaman gaggawar da aka yi, an yanke shawarar cafke Maina a duk inda jami’an hukumar suka gan shi, a yanzu haka jami’an hukumar na mamaye da duk inda aka san Maina ka iya zuwa.

Hukumar ta EFCC ta nuna bacin ranta da yadda wasu manyan jami’an gwamnati ke yi mata zagon kasa a aikin da take yi na kama barayin gwamnati, musamman Maina wanda yansandan Duniya, INTERPOL ke nemansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kokarin yaki da almundahana na hukumar EFCC, kalla a Legit.ng TV

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel