Wa iyathu bilLah: Dan shekara 50 ya fyade 'yar shekara 3 har lahira

Wa iyathu bilLah: Dan shekara 50 ya fyade 'yar shekara 3 har lahira

- Har yanzu dai an kasa magance yiwa yara fyade a kasar Hausa

- Wannan mutumi ya ja yarinyar zuwa wani kango

- Ta cika bayan an garzaya da ita asibiti

'Yan sandan Katsina sun damke wani mutum a garin Jabiri mai suna Abdullahi Sani a kan ya yi wa wata yarinya 'yar shekara 3 fyade har ta rasa ranta.

Wa iyathu bilLah: Dan shekara 50 ya fyade 'yar shekara 3 har lahira

Abdullahi Sani Hoto daga Vanguard

Mai magana da yawun bakin 'yan sandan Katsina, DSP Gambo Isah, ne ya ke gayawa manema labarai a ranar Litinin din da ta gabata. Yace an kama Sani a ranar 12 ga watan Oktoba.Yace Sani ya ja yarinyar ne zuwa wani kango, a inda yayi mata fyaden.

DUBA WANNAN: Kotu ta bayar da umarnin kwace wasu kadarorin alfarma 14 mallakar tsohon ministan Abuja Bala Mohammed

Da aka kama shi an garzaya da yarinyar asibitin Funtuwa Janaral, daga bisani ta ce ga garinku.

Sani ya amsa laifin sa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel