Buhari na kaunar 'yan Igbo - Lai Mohammed

Buhari na kaunar 'yan Igbo - Lai Mohammed

- Lai Mohammed yace shugaba Buhari na matukar kaunar yan Igbo kamar ko wani dan Najeriya

- Ya ce akwai manyan mukamai da yan kabilar Igbo ke rike da su wanda hakan na nuna cewa ba'a ware su ba

Ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kaunar yan kabilar Igbo kamar kowa domin suma yan Najeriya ne.

A cewar sa shugaban kasar bai ware su ba a mulkin kasar kamar yadda suke ikirari, ya kuma bayyana cewa idan akayi duba ga ministoci na gwamnatin Buhari, akwai yan kabilar Igbo a cikinsu, sannan dukkansu suna rike ne da manyan makamai.

Buhari na kaunar 'yan Igbo - Lai Mohammed

Buhari na kaunar 'yan Igbo - Lai Mohammed

Misali yace minstan harkokin waje dan Igbo ne wanda ya fito daga jihar Enugu, haka kuma ministan Ciniki da masana’antu ma dan kabilar Igbo ne da ya fito daga jihar Abia, har ila yau ministan wadago dan asalin jihar Anambra ne.

KU KARANTA KUMA: Atiku Abubakar ya musanta rabon buhuhunan shinkafa saboda 2019

Ya cigaba da cewa karamin ministan Ilimi daga jihar Imo ya fito, don haka da ace shugaba Buhari baya kaunarsu da bai nada ko daya daga cikin su a kan wadannan mukamai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel