Nigerian news All categories All tags
Gwamnan jihar Kaduna ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan maigayi AVM Mohammad

Gwamnan jihar Kaduna ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan maigayi AVM Mohammad

Gwamnan jihar Kaduna ya aika sakon ta’aziyarsa ga yan uwan marigayi tsohon gwamnan jihar Kaduna, AVM Mohammad Mouktar wanda yayi wafati jiya Lahadi a birnin Landan.

A wani jawabi da mai magana da yawun gwamnan, Samuel Aruwan, ya saki, Malam Nasir El-Rufai yace:

Gwamnan jihar Kaduna ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan maigayi AVM Mohammad

Gwamnan jihar Kaduna ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan maigayi AVM Mohammad

“ Na samu labarin mutuwan AVM Mohammad cikin takaici da mika kai ga Allah. Ya kasance tsohon gwamnanmu na mulkin soja wanda yayi aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a jiharmu.

KU KARANTA: Dan bindiga ya buɗe wuta a wata jihar Amurka, mutane 50 sun mutu, 200 sun samu raunuka

A madadin gwamnati da mutanen jihar Kaduna, muna mika sakon ta’aziyarmu ga iyalansa na kusa, abokan arziki. Allah ya jikansa da rahama, Amin.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Zan kayar da Buhari a zaben 2019 - Fayose, Kalli bidiyon:

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel