Buhari ya nuna kiyayyar da yake ma yan kabilar Igbo - Ozekhome

Buhari ya nuna kiyayyar da yake ma yan kabilar Igbo - Ozekhome

- Cif Mike Ozekhome ya soki jawabin da shugabna kasa Buhari yayi a ranar yancin kai

- Lauyan yace shugaban kasar ya gaza magance muhimman al’amura

- Ya zarge shi da tsanar yan kabilar Igbo

Cif Mike Ozekhome wanda ya kasance lauyan tsarin mulki kuma mai kare hakkin dan adam ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya nuna tsanar da yake ma yan kabilar Igbo.

Vanguard ta rahoto cewa a wata sanarwa daga lauyan a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, ya soki jawabin shugabna kasa na ranar yancin kai inda yace ya tabbatar da tsanar da yake ma kabilar Igbo.

Lauyan yayi mamakin dalilin da yasa shugaban kasar bai soki ayyukan Fulani makiyaya da kuma wa’adin barin gari da aka ba Igbo a arewa ba.

Ozekhome yace shugaba Buhari ya gaza amfani da damar wajen magance muhimman al’amura da gwamnatin sa ke fuskata.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi rashin gaskiya a jawabinsa na ranar yancin kai – Junaid Mohammed

A halin da ake ciki, Junaid Mohammed wanda ya kasance dan majalisa a jumhuriya ta biyu ya caccaki jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a ranar yancin kai inda ya zarge shi da karya akan tsare-tsaren sa na harkar noma.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa dan majalisar na maida martani ne ga jawabin da shugaban kasar yayi a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba.

Muhammad yace babu wani abu na musamman tattare da jawabin shugaban kasar sannan kuma cewa ya ma yi rashin gaskiya a ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel