Fadar Aso Rock ta saki muhimman abubuwa 57 da Buhari yayi a lokacin da ake bikin cikar Najeriya 57

Fadar Aso Rock ta saki muhimman abubuwa 57 da Buhari yayi a lokacin da ake bikin cikar Najeriya 57

- A bikin cikar Najeriya 57 da samun 'yancin kai, a yau Fadar Aso Rock ta saki muhimman abubuwa 57 da Buhari yayi a lokacin da ake bikin cikar Najeriya 57

- Murna Bikin cika Najeriyya Shekara 57, fadar shugaban kasa ta kidayo wasu cigaba da aka samu a Mulkin Buhari

- Sai a 1960 Najeriya ta fara mulkar kanta da kanta

Shekaru 57 kenan cur da aka sami 'yancin kai daga mulkin mallaka na turawa, wanda ya faro tun 1914, bayan da aka tumbuke kananan daulolin yankunan da ke cin gashin kansu daga yankin arewa da kudu, aka kuma hade su duka suka tashi a matsayin kasa daya, a abun da ake kira amalgamation.

Fadar Aso Rock ta saki muhimman abubuwa 57 da Buhari yayi a lokacin da ake bikin cikar Najeriya 57

Fadar Aso Rock ta saki muhimman abubuwa 57 da Buhari yayi a lokacin da ake bikin cikar Najeriya 57

"A lokacin da nake matashin soja, na ba da gudummuwata tun daga farko har karshen yakin (Basasar Najeriya) wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum kimanin miliyan biyu, ya kuma haddasa azaba da barna mai yawa," in ji Shugaba Buhari.

Fadar Shugaban kasa ta Lissafo wasu manya-manyan cigaba da aka samu a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari tunga harkar tsaro da kuma Tattalin arzikin kasa.

"Dole mu gode wa zakakuran sojojinmu kan yadda suka fatattaki 'yan Boko Haram, suka samu nasara a kansu kuma rage yawan hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba." Daga nan ya ci gaba da cewa "ba za mu yi kasa a gwiwa ba." Ya ce an fara fadada aikin rundunar Lafiya Dole da take aiki a yankin arewa-maso-gabashin kasar.

A yaki da ta'addanci, shugaban ya yabawa sojin kasar nan, ya kuma yi murna da kwato yan matan chibok da aka yi a baya, tare da alwashin kwato sauran nan gaba kadan.

DUBA WANNAN: Masarautun gargajiya a arewacin kasar nan

"Gwamnati za ta taimakawa dakarun kasar nan ba kawai a yaki da ta'addanci ba, amma har da matsalolin satar mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da kuma rikicin makiyaya da manona," a cewarsa.

Shugaban ya bayyana shirye-shiryen da gwamnatinsa take yi wajen ganin kasar ta rage dogaro kasokan kan man fetur.

A yanzu dai kasar nan ta Najeriya ita ce a baya cikin sa'anninta kasashe da suka sami 'yanci lokaci guda. Sauran sun kere mata a fannin hadin kai na 'yan kasa, zama lafiya, da kuma karfin tattalin arziki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel