Nigerian news All categories All tags
Tabarbarewar yankin Kudu Maso Gabas laifin Buhari ne - Kungiyar kabilar Ibo

Tabarbarewar yankin Kudu Maso Gabas laifin Buhari ne - Kungiyar kabilar Ibo

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kabilar Ibo ta Ohaneze Ndigbo ta na tuhumar shugaban kasa Muhammadu Buhari da nuna banbanci da kuma maishe da al'ummar kabilar Ibo saniyar ware a gwamnatin sa.

Shugaban kungiyar Cif John Nwodo ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai na BBC, inda ya ce wannan abu dai a sarari yake domin kuwa shugaban kasa ya nuna ma su kabilanci.

Akwai rahotanni da suke cewa, Buhari ya sha alwashin nuna kulawarsa ga wadanda suka yi sanadiyar cin zaben sa na shekarar 2015 ta fuskar kada masa kuri'u.

Tabarbarewar yankin Kudu Maso Gabas laifin Buhari ne - Kungiyar kabilar Ibo

Tabarbarewar yankin Kudu Maso Gabas laifin Buhari ne - Kungiyar kabilar Ibo

Cif John ya bayyana cewa, akwai hakkoki da 'yan kabilar Ibo suka cancanta daga wajen shugaban kasa amma saboda bambamcin da gwamnatinsa take nuna wa sai dai su ji a mokobtansu, ya kuma ce hakan ba da cewa ba ne domin kuwa gaba daya kasar Najeriya a karkashin kulawarsa ta ke.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ba zan yi murabus ba - Mugabe

Ya kara da cewa, idan aka yi la'akari da gwamnatin tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari, kuri'un da ya samu daga middle belt kadai sun kere na yankunan Kudu maso Gabas, amma hakan bai sanya shi ya nuna wariya ga wannan yankin ba na kabilar Ibo.

Nwodo ya bayar da misalai ta bangaren harkokin tsaro a yankunan kudu maso gabas, inda ya ce mafi akasarin kwamishinonin 'yan sanda na yankunan kudu maso Gabas 'yan Arewa ne, baya ga cewa basu yankin ciki da wajensa ba.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel