Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

- Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME

- Bayan zana jarabawar Jamb, sai dalibai sun zana ta Post UTME

- Post UTME ita ce take tantance kokarin dalibai masu shiga jami'a

Jami’ar Legas wadda aka fi sani da UNILAG ta fitar da ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME. Ranakun sun kama daga 4 zuwa 6 ga watan Oktoba, 2017..

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME
Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

Rijistra na jami’ar, Dakta Taiwo Ipaye ne ya bada sanarwar cewa dalibai su zo da takaddun shaidar cike jam’iar, daga ranar 28 ga watan Satumba za su iya bugo takaddun daga shafin yanar gizo na jami'ar sannan su zo dakin jarabawar da takardar shaidar shiga jarabawar guda 2.

DUBA WANNAN: Hukumar sojin sama ta kasar Jordan zata hada gwiwa da takwararta ta Najeriya domin yaki da ta'addanci

Ya sake bada sanarwar kai’dojin shiga dakin jarabawar sannan dalibai kar su zo da wayoyin salula dakin rubuta jarabawar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel