Amurka za ta ba Kasar Najeriya gudumuwar kudi

Amurka za ta ba Kasar Najeriya gudumuwar kudi

- Kasar Amurka za ta agazawa Najeriya da makudan kudi

- Amurka za ta raba sama da Dala Miliyan 550 ga wasu kasashe

- Najeriya na cikin kasashen da su ka saba samun taimakon

Labari ya iso mana cewa a bana ma dai Kasar Amurka za ta agazawa Najeriya da makudan miliyoyin kudi kamar yadda aka saba.

Amurka za ta taimakawa wasu Kasashe 4 a Duniya da gudumuwar kudi
Kasar Amurka za ta taimakawa Najeriya

Najeriya na cikin kasashen da za su samu gudumuwa daga Kasar Amurka domin kawo karshen karancin abinci. Shugaban Kungiyar USAID na Amurka da ke taimakawa kasashen Duniya Mark Green ya bayyana wannan a Birnin New York na kasar.

KU KARANTA: Kasashe 9 da ke da makamin nukiliya a Duniya

USAID za ta kashe kudi har Dala Miliyam 550 a kasashen Kudancin Sudan, Yemen, Somalia da kuma Najeriya domin samar da abinci a inda rikici ya auka masu a Duniya. USAID ta dai dade tana wannan kokari a kasashen Duniya har da irin su Kasar Iraki.

A jiya mun ji cewa 'Yan Majalisa na shirin sa kafar wando daya da Kungiyoyi masu zaman kan su a Najeriya kwanan nan da wani kudiri da zai bibiyi yadda Kungiyoyin NGO da CSO ke samun kudi da kuma inda su ke batarwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wasu 'Yan Najeriya sun nuna cewa su na tare da Atiku

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel