Biyafara: APGA ta bayyana yadda za a iya kawo karshen tashin hankali a kudu maso gabas

Biyafara: APGA ta bayyana yadda za a iya kawo karshen tashin hankali a kudu maso gabas

- Wani shugaban jam’iyyar APGA ya bayyana yadda za a kawo karshen tashin hankali a kudu maso gabas

- Shugaban ya yi Allah wadai da gamayyar gwamnonin kudu maso gabashin kasar game da matsayin su a kan kungiyar IPOB

- Shugaban ya daganta tashe tashen hankali a yankin ga rayukan wadanda suka mutu a yakin basasa

Shugaban jam’iyyar adawa ta APGA, Cif Rommy Ezeonwuka, ya yi Allah wadai da gamayyar gwamnonin kudu maso gabashin kasar game da matsayin su a kan kungiyar 'yan asalin yankin Biyafara (IPOB).

Ya ce wannan matsayin ba zai kai ga kawo ƙarshen ayyukanin kungiyar ba.

Ya bukaci gwamnonin su dauki matakan da suka dace don kawo karshen yunkurin tashin hankali a yankin kudu maso gabas.

Biyafara: APGA ta bayyana yadda za a kawo karshen tashin hankali a kudu maso gabas

Shugaban jam’iyyar APGA, Cif Rommy Ezeonwuka

Da yake jawabi ga manema labarai a Oba, Idemili ta masarautar kudu a jihar Anambra, shugaban zamantakewa na Igbo, ya daganta fafutukar kafa yankin Biyafara zuwa ga rayukan wadanda suka mutu a yakin basasa da aka yi ba tare da wani kyakyawar jana’aza ba.

KU KARANTA: Biyafara: Gwamnatin tarayya ta binciko wani asusun bankin IPOB a kasar Faransa

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Ezeonwuka, ya ce: "Saboda haka, ina kira ga gwamnonin jihohin tsohuwar yankin gabashin kasar don hada kai da kawo ƙarshen wannan tashin hankali ta hanyar kafa wani abin tunawa ga sojojin Biyafara wadanda suka mutu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel