Bayafra: Kungiyar ECA zata karrama Nnamdi Kanu a watan Octoba

Bayafra: Kungiyar ECA zata karrama Nnamdi Kanu a watan Octoba

- Kungiyar ECA zata karrama Nnamdi Kanu a watan Octoba bisa gwagwarmayar da yayi na kawo garambawul

- Kanu ya amince da garambawul din ne bayan Farfesa Ben Nwabueze ya shawo kan sa

- Kanu kuma ya amince cewa kungiyar IPOB bazatayi katsalandan cikin zaben da za'ayi a jihar Anambra ba

Wata kungiyar yankin gabashin Najeriya mai suna 'Eastern Consultative Assembly' (ECA) ta bayyana shirye-shiryen ta na karrama shugaban IPOB, Nnamdi Kanu a watan Octoba.

Za'a karrama Kanu ne a wajen kaddamar da wani litaffi da akayi wa take da ''How Nnamdi Kanu Restructured Nigeria'', ma'ana yadda Nnamdi Kanu yayi wa Najeriya garambawul.

Wannan yayi daidai da maganar wani malamin addinin Kirista Evanglist Elliot Ugochukwu-Uko na kungiyar 'Igbo Youth Movement' inda yace Farfesa Ben Nwabueze ne ya shawo kan Nnamdi Kanu har ya amince da garambawul din.

Bayafra: Kungiyar ECA zata karrama Nnamdi Kanu a watan Octoba

Bayafra: Kungiyar ECA zata karrama Nnamdi Kanu a watan Octoba

A cewar mataimakiyar shugaban kungiyar ECA, Uwargida Maria Okwor, kungiyar ECA ne ta wallafa litafin kuma litafin kuma yana dauke da bayyanai akan gwagwarmaya da sadaukar da kai da wasu yan Najeriya sukayi domin ceto kasar daga halaka ta hanyar yin garambawul zuwa hanyar raba dai-dai na adalci.

Uwar gida Okwor da kara da cewa littafin yayi nazari akan gwagwarmayar mazajen jiya kamar su mariyagayi Anthony Enaharo, Marigayi Abraham Adesanya, Marigayi Rotimi Willims, Marigayi Tunji Braithwaite da sauransu wajen kawo garambawul a tsarin mulkin Najeriya.

DUBA WANNAN: Zartar da hukuncin ta'addanci akan IPOB: Kanu ya kaluballanci hukuncin da kotun koli ta zartar

''Littafin yayi bayani kan yadda wasu azzalumai suka dakile rahotanin tarukan kasa da akayi a shekarun baya domin dai su cigaba da cin karen su babu babbaka.

''Kanu ya cacanci yabo saboda ya zaburar da ''yan Najeriya yin garambawul a cikin shekaru 2, abunda yake da kamar wuya a baya.

''A halin yanzu kungiyoyi da yawa sun kafa kwamiti domin jin ra'ayin al'ummar su akan garambawul din, babu shakka yaran da zamu haifa nan gaba zasu gode ma Nnamdi Kanu bisa wannan gagarimin canjin da ya kawo.'' Inji ta.

Kanu ya amince da shawarar da Farfesa Nwabuze ya bashi amma yace zaiyi shawara da sauran mahukuntan kungiyar IPOB din na gida da waje domin su tsayar da magana. Ya kuma amince cewa kungiyar IPOB bazatayi katsalandan cikin zaben da za'ayi a jihar Anambra ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel