Biyafara: Nnamdi Kanu da ayyukan IPOB na sanya rayukan yan Igbo miliyan 11 cikin hatsari – Gwamna Ikpeazu

Biyafara: Nnamdi Kanu da ayyukan IPOB na sanya rayukan yan Igbo miliyan 11 cikin hatsari – Gwamna Ikpeazu

- Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya bayyana cewa ayyukan yan kungiyar IPOB ya sanya rayukan mutane miliyan 11.6 cikin hatsari

- Ya bayyana cewa baza’a saka yan Igbo dake zaune a wajen kudu maso gabas cikin hatsari ba saboda fafutukar kungiyar IPOB

- Gwamnan ya ba da tabbacin cewa ko wani yanki na Najeriya a tsare yake ga kowa harma da yan Igbo domin su cigaba da gudanar da kasuwancin su da harkokin su

Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya kaddamar da cewa ayyukan yan kungiyar Biyafara (IPOB) karkashin shugabancin Nnamdi Kanu ya sanya rayukan yan Igbo miliyan 11.4 dake zaune a wajen kudu maso gabas cikin hatsari.

Ya bayyana cewa baza’a saka yan Igbo dake zaune a wajen kudu maso gabas cikin hatsari ba saboda fafutukar kungiyar IPOB

Legit.ng ta tattaro cewa Ikpeazu ya ba da tabbacin cewa yan Igbo na da damar gudanar da kasuwancin su a ko wani yanki na kasar yayinda yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa dake buja.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kasar Faransa ta karyata danganta ta da IPOB, da kuma Nnamdi Kanu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar Ohanaeze Ndigbo, wacce aka fi sani a matsayin na dattawan mutanen kabilar Igbo a Najeriya ta bayyana cewa karda a bari kasar ta kara shiga wani yakin basasa.

Mambobin kungiyar sun kuma bayyana cewa basa ra’ayin rabewa amma suna son daidaito da adalci daga shugabannin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel