An yanke mata hukuncin wata 6 a gidan kaso saboda satar waya

An yanke mata hukuncin wata 6 a gidan kaso saboda satar waya

- Mai karamar sata a Nakeriya shine ke fadawa cikin wahala. Mai babbar sata kuma sai da a yi masa mubayi'a

- Raji ta saci waya da laftof a Osogba, jihar Ogun

- Alkali ya yanke hukuncin wata 6 a gidan yari ko kuma ta biya tara

Wata kotu a Osogbo, a jihar Osun, ta yanke wa wata mata ’yar shekara 35 hukuncin zama har tsawon wata 6 a gidan kaso saboda ta saci wayar salula.

An yanke mata hukuncin wata 6 a gidan kaso saboda satar waya
An yanke mata hukuncin wata 6 a gidan kaso saboda satar waya
Asali: Depositphotos

Wanda ya shigar da karar kotun, Sifeto Joshua Oladoye, ya ce wa alkalin, Nafisat Raji ta saci wayar salula kirar Techno Y6 ta wata Deborah Akindele, wacce kudin ta ya kai N14,500 a titin Fayemi, sannan kuma ta kara satar wata laftof kirar HP ta wani Mubarak Olabopo, wanda ita kuma kudin ta ya kai N45,000 a 30 ga watan Agusta, 2017, a titin Akeji, a Osogbo.

Akalin da ya saurari karar ya ce Raji ta keta haddin sashe na 412,383 ta kuma cancanci hukunci na sashe 309(9) daga kundin tsarin laifuka na jihar Osun.

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun kashe 2, sun raunata soja a Benuwe

Raji ta fashe da kuka inda ta amsa laifukan ta. Sannan ta roki kotu ta ji kan ta.

Majista Adenike Olowolagba ya yanken hukuncin yin wata 6 a kidan kaso ko kuma ta biya tarar Naira 3000.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel