Sabuwar shekarar Musulunci : Gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu a ranar Juma’a dan murnar shiga sabuwar shekara

Sabuwar shekarar Musulunci : Gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu a ranar Juma’a dan murnar shiga sabuwar shekara

- Gwamnatin Kani ta bada hutu rana daya dan murnar shiga sabuwar shekarar muslunci

- Farfesa Hafiza Abubukar ya taya al'ummar Kano da duniya baki daya murnar shiga sabuwar shekara

- Ranar shiga sabuwar shekarar muslunci wannan shekara yayi daidai da ranar bikin samun yancin Najeriya

Gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu a ranar Juma’a 22 ga watan Satumba domin nuna murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Wannan sanarwar yafito ne daga bakin kwamishinan watsa labaru, Mallam Muhammad Garba a ranar Laraba lokacin da ya zanta da manema labaru.

Sabuwar Shekarar Musulunci, wanda shine wata na farko a cikin kalandar Islama, yayi dai da ranar bikin da Najeriya ta samu yanci kai.

Sabuwar shekarar Musulunci : Gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu a ranar Juma’a dan murnar shiga sabuwar shekara

Sabuwar shekarar Musulunci : Gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu a ranar Juma’a dan murnar shiga sabuwar shekara

Mataimakin gwamnan jihar Kano farfesa Hafiz Abubakar yana taya musulman jihar da na duniya baki daya murnar shiga sabuwar shekarar musulunci.

KU KARANTA : Mutun daya ya rasa ran sa a Kaduna yayin da yansanda suka yi masanya wuta da masu garkuwa da mutane

Abubakar yayi kira da al’ummar Kano da su yi amfani da wannna hutu wajen yiwa Najeriya adu’ar zaman laifya.

Yayi kira da yan Najeriya da su mara wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya wajen gina da cigaban kasa.

Legit.ng ta rawaito cewa, ranar Juma’a 22 ga watan Satumba shine 1 ga watan Muharram na kalanadar Musulunci na shekara 1439 bayan hijira.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel