Rikicin IPOB: Ýan Arewa sun tsere daga garin Umuahia

Rikicin IPOB: Ýan Arewa sun tsere daga garin Umuahia

Da dama daga cikin shagunan Hausawa da sauran kabilun Arewa dake kasuwanci a jihar Abia sun rufe shagunansu a ranar Talata 12 ga watan Satumba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Har ma yan baro, masu dakon kaya ba’a hange su akan titunan garin ba, kai har da babban Masallacin garin dake kan hanyar zuwwa garin Owerri na jihar Imo, babu kowa a wajen.

KU KARANTA: Ka daina nuna kwaɗayinka a fili, ba haka ake zama shugaban ƙasa ba – Gwamna Kashim ga Atiku

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon gudun kai musu hare hare daga yayan kungiyar rajin samar da kasar Biyafara, IPOB musamman yayin da suke fafatawa da Sojoji.

Rikicin IPOB: Ýan Arewa sun tsere daga garin Umuahia
Rikicin IPOB

A hangi matasan IPOB suna ta yawo a cikin garin Umuahia suna wake waken yaki, cikin motoci da dama suna balle shagunan Hausawa sai dai Sojoji sun cigaba da yawo a titunan garin domin tabbatar da doka da oda.

A nasa bangaren, Sarkin Umuahi, Eze Philip ya shawarci gwamnati data nemi sulhu da yan IPOB, ba wai yin amfani da karfin tuwo ba, don a ganinsa, hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel