An zargi magoya bayan Kwankwaso da laifin tada tarzoma a Kano

An zargi magoya bayan Kwankwaso da laifin tada tarzoma a Kano

- 'Yan Sanda sun zargi 'Yan Kwankwasiyya da laifin tada rikici a Kano

- An yi hatsaniya a lokacin Bikin Hawan Sallah a Garin Kano kwanaki

- Hukuma ta daura laifin a kan magoya bayan tsohon Gwamna Kwankwaso

Jami'an tsaro sun ce mutanen Sanata Rabiu Musa Kwankwaso su ka jawo rikicin da ya barke a lokacin hawan daushe kwanaki.

An zargi magoya bayan Kwankwaso da laifin tada tarzoma a Kano

Tsohon Gwamna Kwankwaso da Dr. Ganduje

'Yan Sanda sun daura laifin mummunar arangamar da aka samu tsakanin mutanen Ganduje da Kwankwaso a kan magoya bayan tsohon Gwamna Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso inda su kace magoya bayan Kwankwasiyyar ne su ka dauko Jama'a domin kawo rudani a filin hawan daushe.

KU KARANTA: Manyan PDP sun kai ziyara wajen ambaliya

An zargi magoya bayan Kwankwaso da laifin tada tarzoma a Kano

Gwamnan Jihar Kano Ganduje

Jami'in 'Yan Sanda Rabiu Yusuf da yayi magana a madadin Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Kano yace 'Yan Kwankwasiyyar sun fito ne su na ihun 'Ba ma yi' a lokacin da Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje yake kokarin zuwa wajen hawan daushe da tawagar sa.

An yi hatsaniya kwarai da gaske a lokacin na Bikin Hawan Sallah inda aka ji wa jama'a da yawa rauni. 'Yan Sanda sun yi gargadi da a guji kawo irin wannan rikici a Garin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Neman aiki na da wahala a Najeriya?

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel