Har yanzu ana cikin takun-saka tsakanin Neymar da Barcelona

Har yanzu ana cikin takun-saka tsakanin Neymar da Barcelona

- Rikicin Barcelona da tsohon Dan wasan ta ya ki karewa

- Ana ta cacar baki tsakanin Neymar da Kungiyar Barca

- Barcelona tace matashin Dan wasa Neymar ya ci amanar ta

A halin yanzu rikicin Kungiyar Barcelona da tsohon Dan wasan ta na kasar Brazil Neymar na kara zafi.

Har yanzu ana cikin takun-saka tsakanin Neymar da Barcelona
Dan wasa Neymar ya koma PSG daga Barcelona

Da alama takkaddamar da ke tsakanin Dan wasan da tsohon Kulob din nasa ya ki ci ya kuma ki cinyewa bayan da Shugaban Kulob din Josep Maria Bartomeu yace Neymar da kuma Mahaifin sa sun yaudari Barcelona bayan an aminta da su.

KU KARANTA: Watakila kasar Syria ta tafi Gasar 'World Cup'

Bartomeu yace tafiyar Neymar din ba zata bai yi masu dadi ba wanda aka dauki dogon lokaci ana ta surutu a kai. Shugaban Kungiyar yace hakan ya sa neman wanda zai maye gurbin Dan wasan cikin san lokaci yayi wahala.

Dan wasa Neymar dai ya maida martani ta shafin sa na Instagram inda yayi kaca-kaca da Shugaban Kungiyar inda yace shi Josep Maria Bartomeu bai san abin da yake yi ba. Ba dai yau Neymar ya fara sukar Shugabannin Kungiyar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da wasan Super Eagles da Kamaru

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel