Abin da Shugaba Buhari ya fadawa mai-kwaikwayon sa MC Tagwaye

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa mai-kwaikwayon sa MC Tagwaye

- Mai kwaikwayon Shugaban kasa Buhari ya gana da shi a Daura

- MC Tagwaye ya bayyana yadda su ka yi da Shugaban kasar

- Bisa dukkan alamu Bawan Allah masoyin Shugaba Buhari ne

Kwanan nan Shugaban kasa Buhari ya gana da Jama'a da su ka kai masa ziyara a Daura lokacin Sallah.

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa mai-kwaikwayon sa MC Tagwaye

Shugaba Buhari da mai-kwaikwayon sa MC Tagwaye

NAIJ Hausa sun kawo maku abin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa mai-kwaikwayon nan na sa MC Tagwaye a lokacin da su ka hadu a Garin Daura. Tagwaye ya bayyana wannan ne a shafin sa na Facebook.

KU KARANTA: Obasanjo na shirin tsaida El-Rufai Shugaban kasa

MC Tagwaye wanda masoyin Shugaban kasar ne na gidi yace bayan sun shiga dakin da gwarzon na sa yake sai Shugaba Buhari yace ga shi ya ci katuwar babbar riga kuma dauke da taswirar Kasar Najeriya da kuma Jihar Katsina a jikin ta alamar ya cika dan kasa mai kishi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin ganin 'Yan Najeriya sun ji dadi a mulkin sa. Shugaba Buhari ya bayyana wannan ne a gidan sa a Daura.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Biyafara sun yi alwashin kare Nnamdi Kanu

Source: Legit Newspaper

Online view pixel