Karya ne, babu kwamandojin mu da aka kama - Shekau (bidiyo)

Karya ne, babu kwamandojin mu da aka kama - Shekau (bidiyo)

Shugaban kungiyar jama’atil ahlus Sunnah li dda’awati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabuwar bidiyo ranan Asabar washe garin Sallah

Yayi doguwar jawabi a wannan bidiyo inda ya fara da kuduba da yaren larabci kafin Hausa.

Yace: “Naji kun ce ku kama yan uwan mu 70, karya ne, kun ce kun kama kwamandojin mu 5, bamu tura kowa ba, muna nan da kwamandojin mu muna aiki.”

KU KARANTA: An yi hawa saboda murnar samun lafiyar Shugaba Buhari a Daura

“Kun ce zaku kama cikin kwanaki 40 kuma yau ne kwana 40 din, gani nan kuma mun ci Sallah lafiya, Shekau na nan."

“Buratai in kara maimaitawa, kwanaki 40 din sun wuce, ku je ku sake shiri. Kai kuma Sheka, ka cigaba da sheka karya, Allah zai sheka ka.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Online view pixel