Bayan karewan wa’adin kama shi, Shekau yayi isgili ga Buratai (sabuwar bidiyo)

Bayan karewan wa’adin kama shi, Shekau yayi isgili ga Buratai (sabuwar bidiyo)

- Shugaban Boko Haram ya saki sabuwar Bidiyo

- Ya yi isgili akan gazawa wajen kama duk da wa'adin da aka bada

Shugaban kungiyar jama’atil ahlus Sunnah li dda’awati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabuwar bidiyo ranan Asabar washe garin Sallah.

Yayi doguwar jawabi a wannan bidiyo inda ya fara da kuduba da yaren larabci kafin Hausa. Shekau yayi isgili ga shugaba hukumar sojin kasan Najeriya akan gazawar kama shi duk da wa’adin kwana 40 da ya bada.

Bayan karewan wa’adin kama shi, Shekau yayi isgili ga Buratai (sabuwar bidiyo)
Bayan karewan wa’adin kama shi, Shekau yayi isgili ga Buratai (sabuwar bidiyo)

Yace: “Kun ce zaku kama cikin kwanaki 40 kuma yau ne kwana 40 din, gani nan kuma mun ci Sallah lafiya, Shekau na nan."

“Buratai in kara maimaitawa, kwanaki 40 din sun wuce, ku je ku sake shiri.”

KU KARANTA: An rasa inda makaman Jami'an tsaro su ka shige a Najeriya

Kana ya caccaki kakakin hukumar soji, Janar Sani Usman Kukasheka, inda ya kira sa makaryacin banza.

Yace: “Kai kuma Sheka, ka cigaba da sheka karya, Allah zai sheka ka.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel