Wa zai cika mata burin ta: Wata yarinya na nema ta ga Shugaba Buhari

Wa zai cika mata burin ta: Wata yarinya na nema ta ga Shugaba Buhari

- Wata yarinya karama ta aikawa Shugaba Buhari takarda

- Wannan yarinya tace burin ta ganin Shugaban kasar Buhari

- Aisha Aliyu ta fito ne daga Jihar Bauchi a Arewacin Najeriya

Mun samu labari cewa wata yarinya 'yar shekara 10 ta aikawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasika cewa tana so ta gan shi.

Wata 'yar shekara 10 ta rubutawa Shugaba Buhari wasika; ina so in gan ka

Wasika zuwa ga Shugaba Buhari

Wannan yarinya mai suna Aisha Aliyu Gebi daga Jihar Bauchi a Arewa maso gabashin kasar ta fara wasikar ne da tambayar halin lafiyar Shugaban kasar a yanzu wanda daga nan tace abin da ya sa ta rubuta takardar shi ne tana kaunar ganin Shugaban kasar fuska da fuska.

KU KARANTA: Rarara ya nishadantar da masoya Buhari a Bauchi

Wata 'yar uwar ta ce mai suna Hasna Gebi ta yada wannan takarda a shafin ta na Tuwita kuma tuni har daya daga cikin Hadiman Shugaban kasar Malam Bashir Ahmad ya nemi zantawa da wannan mata goggon yarinyar. Watakila dai a cika mata burin ta na ganin Shugaban kasa.

Kwanaki kun ji kamar dai yadda kowa yake gani ba shakka rashin lafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na iya hana sa takara a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Beraye sun fatattaki Shugaba Buhari

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel