Yakassai, Waku, Tsav da sauran su sun bukaci gwamnatin tarayya ta tsare Nnamdi Kanu

Yakassai, Waku, Tsav da sauran su sun bukaci gwamnatin tarayya ta tsare Nnamdi Kanu

- Shugabannin Arewa sun bukaci gwamnatin tarayya da ta sake kama shugaban kungiyar IPOB

- An zargi Nnamdi Kanu da ketare sharuddan beli da kotu ta gindaya masa

A jiya Litinin, 28 ga watan Agusta wasu shuwagabannin kungiyoyin Arewa da Arewa ta Tsakiya sun fadawa Gwamnatin tarayya cewa a sake kama shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu saboda ketare wasu sharrudan beli da kotu ta gindaya masa.

Tanko Yakasai ya bayyana cewa shawara da gwamnatin tarayya ta yanke na sake kame Nnamdi Kanu abu ne da ya dace.

Yakasai ya fadawa jaridar Vanguard cewa an ba shugaban IPOB beli ne a kan wasu sharruda, ya kara da cewa idan ya kasance bayyane cewa ya ketere sharrudan beli, kotun ce zata dauki mataki.

Yakassai, Waku, Tsav da sauran su sun bukaci gwamnatin tarayya ta tsare Nnamdi Kanu
Yakassai, Waku, Tsav da sauran su sun bukaci gwamnatin tarayya ta tsare Nnamdi Kanu

A cewarsa, balaifi bane idan gwamnatin tarayya ta dauki mataki kan hakan, ya kara da cewa: “Kanu ya kasance karkashin beli bisa wasu sharruda da idan aka ketare su, ba laifi bane gwamnati ta ta nemi shawarar kotu kan irin mataki da zata dauka."

KU KARANTA KUMA: Kungiyar NLC ta bukaci ayi kakkaba a majalisar Buhari

Da yake Magana a kan al’amarin, mamban kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF, Sanata Joseph Waku, yayi kira ga hukuma da ta sake kame shugaban IPOB cikin gaggawa. Waku a wata tattaunawa da yayi da jaridar Vanguard a daren jiya, yace babu wanda ya fi karfin doka, ya kara da cewa Nnamdi Kanu ma bai fi karfin ta ba.

A bangaren sa, Tsohon kwamishinan yansanda, Alhaji Abubakar Tsav, yace: ba’a sauke wasu laifuffuka dake kanshi ba; an dai sake shi ne bisa dalilin rashin lafiya. Dalilin da ya sa kotu ta bashi sharruda kuma ya ketare su. Sannan yana neman ta da zaune tsaye.

Shugaban Coalition for Governance and Change Initiative, Okpokwu Ogenyi, ya shawarci shugaban IPOB da ya roki mutanen Najeriya da Gwamnatin ta saboda ketare shurruda da aka bashi.

Shugaban kunhiyar Miyatti Allah , Alhaji Garus Gololo, ya bayyana ra’ayinsa cewa kada hukumomi su bari al’amarin ta gagaresu wajen gudanar da ayyukan su yanda ya kamata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel