Yajin aikin Jamia'ar LAUTECH ya kusa zuwa karshe

Yajin aikin Jamia'ar LAUTECH ya kusa zuwa karshe

- Yajin aikin Jamia'ar LAUTECH ya kusa zuwa karshe

- Shugaban Jamia'ar ne ya bayyana wannan kwanan nan

- An dai dade Dalibai na zaune a gida ba karatu a Jami'ar

Shugaban Jamia'ar LAUTECH yace yajin aikin Jamia'ar LAUTECH din ya kusa zuwa karshe nan ba da dadewa ba.

Yajin aikin Jamia'ar LAUTECH ya kusa zuwa karshe

Jamia'ar LAUTECH ta Ogbomosho

Farfesa Oladapo Afolabi wanda shi ne Shugaban Jamia'ar fasahar ta Ladoke Akintola da ke Ogbomosho yace 'Yan Makarantar za su koma Makarantar kwanan nan don kuwa an kusa shawo kan rikicin da ake ciki.

KU KARANTA: Wani ya kusa kashe kan sa don talauci

Kamar yadda mu ka ji daga Jaridun Kasar nan bayan an ci dogon zaman gida za a bude Jami'ar kwanan nan. Majalisar gudanarwar Jami'ar tace ana zama ba dare ba rana domin kawo karshen yajin da an dade ana yi ko da ba ta fadi ranar ba.

Kwanaki ku ka ji cewa an kama hanyar shawo karshen yajin aikin ASUU bayan da Ministan Ilmi ya amince da laifin su. Ministan yace: Mu muka saba alkawarin da aka yi a baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dubi yadda farashin kaya su ka zama

Source: Legit

Online view pixel