Jama'a sun yi tir da Hukumar JAMB da ta rage matakin zuwa Jami'a

Jama'a sun yi tir da Hukumar JAMB da ta rage matakin zuwa Jami'a

- A bana da maki 120 sai ka shiga Jami'a a Najeriya

- Hukumar JAMB ta rage makin da ake bukata bana

- An yi tir da wannan su na cewa makin yayi kadan

Idan ku na bin mu za ku ji cewa an saukar da makin shiga Jamia'a a Najeriya wannan shekarar a wannan makon.

Jama'a sun yi tir da Hukumar JAMB da ta rage matakin zuwa Jami'a
Masu zana jarrabawar JAMB a daki

Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar zuwa Jami'a a Najeriya tace a shekarar bana da maki akalla 120 cikin 400 sai mutum ya samu shiga Jami'a a Najeriya. An dauki wannan mataki ne bayan Jama'a da dama sun fadi jarrabawar da aka zana kwanaki.

KU KARANTA: An soki masu bikin dawowar Buhari

Jama'a da dama sun yi tir da wannan mataki su na cewa makin yayi matukar kadan. Wasu sun ce idan har aka rika daukar masu maki 120 cikin 400 babu yadda za ayi a yaye daliban kirki a Kasar da za su yi wani abin a zo a gani kamar yadda takwarorin su ke yi a Duniya.

A baya mun fadu maku cewa Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantu na gaba da Sakandare a Kasar za ta rage makin da ta saka a baya na samun shiga Jami’o’in Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana bukatar tsaro a coci?

Source: Legit

Online view pixel