Dawowar Shugaba Buhari; Ji me Asari Dokubo ke cewa cikin shagube (Bidiyo)

Dawowar Shugaba Buhari; Ji me Asari Dokubo ke cewa cikin shagube (Bidiyo)

- Mujadihi Asari Dokubo, dan raji da babatun kare hakkin yankin kudancin Najeriya ne, wanda tun zamanin mulkin Obasanjo yake karadi da cika baki kan lallai sai ya kori gwamnatin tarayya daga cin arzikin yankinsu mai arzikin man fetur.

Bayan dawowar shugaba Buhari a jiya, masu tsokaci sun bude kaafensu domin yabawa, murna ko suka da nuna bakin cikinsu. Asari Dokubo ma dai bai bari an barshi a baya ba, ya nadi bidiyo inda yake caccakar magoya bayan Buhari da ma shugaban.

Dawowar Shugaba Buhari; Ji me Asari Dokubo ke cewa cikin shagube

Dawowar Shugaba Buhari; Ji me Asari Dokubo ke cewa cikin shagube

Asari Dokubo ya ce mutane su dena damun jama'a da wata murnar wai Baba ya dawo, amma su nuna fushinsu kan kin gayawa mutan kasar nan cutar da ke damunsa da Buharin yayi.

Ya kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya dena boye-boye kan rashin lafiyar tashi, sannan yace shugaban yayi wa jama'a aikin da suka zabo shi yayi.

DUBA WANNAN: Siyasar Kaduna, kungiya na neman afuwar talakawa kan kawo Malam El-Rufai

Ga link din bidiyon dai da ya dauka a gaban ruwan linkayarsa:

https://web.facebook.com/faith.kirian/videos/1544642812270083/

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel