An yi kira ga Gwamnonin Najeriya su dabbaka dokar kare kananan yara

An yi kira ga Gwamnonin Najeriya su dabbaka dokar kare kananan yara

- Ana kokarin ganin an kafa dokar kare yara kanana a Najeriya

- Mafi yawan Arewacin kasar babu wannan doka a yanzu haka

- Jihohin Kudu ne su ka dabbaka dokar a Yankin su a halin yanzu

Ko ka san cewa da dama na Jihohin Arewa ba a kafa dokar kare hakkin kananan yara ba ta ChildRight.

An yi kira ga Gwamnonin Najeriya su dabbaka dokar kare kananan yara

Arewa babu dokar kare hakkin kananan yara

Kwanan nan Kungiyoyi da dama su kayi wani kira domin tabbatar da cewa Gwamnonin Jihohin Kaduna, Kano, Sokoto da irin su Kebbi sun kafa dokar nan ta ChildRights wanda za ta ba kananan yara kariya daga fyade da cin zarafi da ma toye hakki da damar karatu.

KU KARANTA: Wani yayi kuka bayan dawowar Buhari

An yi kira ga Gwamnonin Najeriya su dabbaka dokar kare kananan yara

Akwai kananan yara da ke bara maimakon karatu

A irin su Jihar Kaduna dai Majalisar Jihar har yanzu ba ta amince da wannan doka ba. A wasu Jihohin ma dai har yanzu ba a gabatar da wannan doka ba sam. Wannan doka ce dai za ta kare dubannin yara da ake yi wa fyade da danne su a bangaren Kasar.

Kwanaki Yan Sanda su ka damke wani tsohon babban Jami'in ta da laifin lalata da karamar yarinya ‘yar shekara 9.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani yace maza su guji ba mata Amala kullum

Source: Legit

Tags:
Online view pixel