2019: Jiga-Jigai 5 na PDP da zasu kara da dan takarar jam'iyya mai mulki ta APC

2019: Jiga-Jigai 5 na PDP da zasu kara da dan takarar jam'iyya mai mulki ta APC

Har yanzu shugaba Muhammadu Buhari bai bayyana aniyarsa ta son sake takara shugabancin Nigeria a kakar zabe ta 2019 ba amma duk da hakan ba za a fitar da zaton zai sake takarar ba musamman ma da ywaitar kiraye - kiraye daga magoya baya da na kusa da shi a kan ya sake fitowa takarar.

A gefe guda, jam'iyyar hamayya ta PDP da ta sha kaye a hannun APC a zaben 2015 ta sha alwashin dawo da mulki hannunta a 2019 kamar yadda jam'iyyar ta bayyana ta bakin jagororin ta a gangamin ta na kwanan nan da ta yi a abuja. (Sharhin Jaridar Daily Trust)

2019: Jiga-Jigai 7 na PDP da zasu kara da dan takarar jam'iyya mai mulki ta APC

2019: Jiga-Jigai 7 na PDP da zasu kara da dan takarar jam'iyya mai mulki ta APC

Ya'ya'n jam'iyyar ta PDP da ke burin gwabzawa da Shugaba Buhari sun hada da;

1. Ahmed Makarfi.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna karo biyu, 1999 zuwa 2003, da 2003 zuwa 2007, tsohon sanata karo biyu, 2007 zuwa 2011, da 2011 zuwa 2015 shekarar da ya sha a hannun jam'iyyar APC a yunkurinsa na komawa majalisar dattijai karo na uku, yanzu kuma shugaban jam'iyyar PDP bayan gwabza dogon rikici tsakaninsa da tsohon shugaban jam'iyyar Ali modu. A kwai kyakykyawan zaton zai ajiye shugabancin jam'iyyar domin yin takarar shugabancin kasa musamman ma da jam'iyyar ta bayyana aniyarta na mika takarar shugabancin kasar ga yankin arewa.

Rawar da ya taka wajen dakile rikicin addini da kuma ayyukan raya kasa da ya shimfida lokacin yana gwamna na daga cikin nagartar da makarfi zai dogaro da su domin yakin neman zabe.

2. Sule LAMIDO

Alhaji sule lamido na daga cikin gogaggun yan siyasa da suka rage a Nigeria, ya kasance daga cikin shahararrun ya'ya'n jam'iyyar PRP da suka zama yan' majalisar kasa a janhuriya ta biyu kafin daga bisani ya zama jigo a jam'iyyar SDP a janhuriya ta uku. Ya rike mukamin ministan harkokin waje karkashin tsohon shugaba obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2003 kafin daga baya ya lashe zaben gwamnan jihar sa ta jigawa a 2007. Tuni dai sule lamido ya fara yakin neman shugabancin kasa a jam'iyyar sa ta PDP bayan da bayyana niyyar sa ta son yin takarar. Ya samu yabo musamman a fannin ayyukan raya karkara da bunkasa ilimi lokacin yana gwamna. Saidai halin zafin kai da rikita - rikita na barazana ga nasarar lamido a siyasance.

KARANTA WANNAN: An gano mummunar aniyar Abubakar Shekau

3. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa tsawon shekaru 8, Atiku na daga cikin sunayen da ke amo a fagen siyasar Nigeria. Atiku bai taba boye kwadayin sa na son ya mulki Nigeria ba domin a baya yayi takara a jam'iyyar ACN a 2007 bayan samun baraka da maigidan sa tsohon shugaba Obasanjo, ya kara yunkurin tsayawa amma ya sha kaye tun a zaben fitar da gwani a hannun tsohon shugaba Jonathan a 2011, a shekara ta 2014 bayan ya canja sheka zuwa jam'iyyar APC ya kara neman takarar amma ya kuma shan kasa a zaben fitar da gwani a hannun shugaba Buhari. Duk da kasancewar har yanzu yana jam'iyyar APC akwai yiwuwar ya kara komawa PDP domin yin takarar shugaban kasa musamman ma da a ka ji shi kwanan nan yana sukar jam'iyyar APC din. Kwanan nan Atiku ya yi murnar cika shekaru 70 da haihuwa, hakan na nuni da cewar zai cika shekara 72 a 2019, kusan za iya cewa ita ce damar sa ta karshe da zai nemi shugabancin Nigeria. Atiku na kokarin ya ga jam'iyyar PDP ta sahalewa yankin arewa maso gabas fitar da dan takara domin saukaka masa samun damar lashe tikitin takarar shugaban kasar.

Yawan canjin sheka da atikun ke yi na iya zamar kalubale ga burin sa na son ya mulki Nigeria.

DUBA WANNAN: Almajirci; kalubalen arewa da musulman Najeriya

4. Ayo Fayose

Ranar 21 ga watan fabarairu na shekarar nan ya bayyana burinsa na son yin takarar shugabancin Nigeria a 2019, wani mataki da yawan jama'a ke gani a matsayin wasa duk da dagewar sa a kan da gaske ya ke a kan kudirin na sa. Tuni dai wasu ke yi wa gwamnan na ekiti dan shekara 56 kirarin "Trump" din Nigeria saboda lafazin sa na katobara. Fayose, ya bayyana cewar shine zai karbi mulki a hannun shugaba Buhari duk da yawaitar gwarazan yan takara da suka fi shi karfi a jam'iyyar ta PDP.

5. David Mark

Sanata David mark, tsohon janar ne na soja, kuma tsohon gwamnan jihar Niger daga shekarar 1984 zuwa 1986 kafin kasancewar sa ministan sadarwa a 1987.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel