Kwana 40 a kamo Shekau, shin me sojin Najeriya suka taka?

Kwana 40 a kamo Shekau, shin me sojin Najeriya suka taka?

- Babban hafsun soja Janar Tukur Buratai ya bawa sojin Najeriya wa'adin kwana 40 a kamo Shekau a mace ko a raye

- Cikin kwanakin Boko Haram ta cigaba da kai hare-hare a jihar Borno

- Sojjin Najeriya suna kokarin kawo karshen ta'addanci a Kasa

A kwanankin baya Legit.ng ta kawo muku labarin Babban hafsun soja, Janar Tukur Buratai da ya bada wa’adin kwana 40 a kamo shugaban ‘yan Boko Haram Abubakar Shekau a mace ko a raye.

Janar Yusuf Tukur Buratai ya bawa Manjo Janar Ibrahim Attahiru, babban kwamandan Operation Zaman Lafiya Dole umarnin yayi duk iya kokarin da zai yi don chafke shugaban ‘yan ta’addan a duk inda yake, wanda hare-haren da suka kai ya jawo sanadiyyar rasa rayuwakan mutane sama da 100,000.

Kwana 40 a kamo Shekau, shin me sojin Najeriya suka taka?
Kwana 40 a kamo Shekau, shin me sojin Najeriya suka taka?

A kwanakin nan Boko Haram ta cigaba da kai hare-hare a Maiduguri da wasu garuruwa a jihar Borno. Umarnin Buratai ba ba kamo Shekau kadai bane, har da kokarin kawo karshen rashin zaman lafiya a kasa.

Tun a 2009 ake bada sanarwar an kama Shekau jina-jina ko an kashe shi, amma har yanzu yana cigaba da sakin bidiyo a yanar gizo. Sojin Najeriya sun bada rahoto a kwanaki na ‘yan Boko Haram suna samun wanda ke bad-da-kama a tsakaninsu yayi shigar Shekau da ake zargin ya mutu.

A 2011, an bada rahoton kashe Shekau a Kano amma sai ya sake sakin faifan bidiyo yana sukar Shugabbanin Najeriya. Akwai jita-jitar mutuwar Shekau da yawa amma sai kwatsam ya fidda sabon bidiyo da yake bayyanna kansa.

DUBA WANNAN: Buhari na nan cikin koshin lafiya

A tsakanin lokacin ne Kasar Amurka ta yi shelar bada ladan kudin dala miliyan 7 ga duk wanda zai kamo Shekau. Haka a 2012, JTF ta bada shelar bada ladan naira miliyan 50 ga duk wanda ya kamo Shekau.

Kwanaki kadan bayan umarnin Buratai aka sami labarin mutuwar ma’aikatan mai da soji a Maiduguri da ‘yan Boko Haram suka kai musu hari. Harin yayi sanadin mutuwar soji, Farfesoshi da ma’aikatan jami’ar Maiduguri.

Faruwar hakan ya sa Mukaddashin Shugaban Kaasa, yemi Osinbajo ya umurci soji da su sake mayar da cibiyarsu zuwa Maiduguri. Da bawa rundunar sojin isassun kayan aiki kamar su kyamarori da zasu gano ‘yan ta’addan daga nesa da suke shirin kai hari .

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel