Majalisa ta ba da umurnin kamo manyan shugabanni 30 a Najeriya

Majalisa ta ba da umurnin kamo manyan shugabanni 30 a Najeriya

- Majalisar dattawa ta ba da umurnin kamun shugabanin kamfanoni 30 a Najeriya

- An rahoto cewa ana zargin shugabannin ne da hannu a zambar kudaden shiga na kimanin naira triliyan 30

- An ba da umurnin kamun ne bayan shugabannin sun ki amsa gayyatar da majalisa tayi masu

A ranar Juma’a 4 ga watan Agusta, majalisar dattawa ba yan sanda umurnin kama shugabannin kamfanoni 30 da ake zargin su da hannu cikin zambar kudaden shiga.

Kamfanoni 63 aka zarga da hannu a cikin zambar kudaden shiga na kimanin naira triliyan 30 sannan kuma majalisar dattawa ta gayyace su amma 33 ne kadai suka amsa gayyatar.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan kwastam, sufuri, Hope Uzodinma ya bayyana kin halartar gayyatar da sauran shugabannin sukayi a matsayin rashin girmama majalisar dokoki sannan kuma y aba da uumrninkama su.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya za ta gyara tituna a jihohin Plateau da Kwara

Ga sunayen kamfanonin da aka ba da umurnin kama shugabanninsu:

1. Crown Flour Mills

2. Glo Mobile

3. British American Tobacco

4. CCECC 5. Dana Group

6. Olam Int. Ltd

7. Hong Xing Steel Co. Ltd

8. Visafone

9. African Wire

10. Star comments and Allied Ltd 11. Aarti Steel Nig. Ltd.

12. Abyem-Diva Int. Ltd

13. Gagasel Int.

14. Friesland Capina

15. Etco Nig.

16 Edic Chemicals and Allied Distributors

17 De United Foods

18. Don Climax Group

19. Skill G NIG Ltd

20. Premium Seafood

21. La Rauf Nig.Ltd.

22. Standard Metallurgical Co. Ltd

23. Kam Industries

24. IBG Investment Ltd.

25. Orazulike Trading Co. Ltd

26. Popular Foods Ltd

27. A-Kelnal Integrated & Logistics Services

28. African Industries,

29. African Tiles and Cermaics

30. ZTE Nigeria

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel