Yanzu-Yanzu: Matasan arewa na cikin ganawa da Ndigbo dake Kano kan wa’adin barin gari

Yanzu-Yanzu: Matasan arewa na cikin ganawa da Ndigbo dake Kano kan wa’adin barin gari

- Wata kungiyar matasan arewa sun hadu da wakilan Igbo

- Kungiyar sun hadu ne don tattaunawa a kan wa’adin barin gari da aka ba kabilar Igbo mazauna arewa

Kungiyar matasan Arewa sun hadu da wakilan Igbo dake zaune a jihar Kano a ranar Juma’a, 4 ga watan Agusta.

Channels TV ta rahoto cewa kungiyar sun hadu ne don tattaunawa a kan rigimar wa’adin barin gari da aka ba mutanen Igbo dake zaune a arewa.

Ku tuna cewa a baya Legit.ng ta rahoto cewa mambobin kungiyar AYCF, sun aika da wata waski inda uska bukaci dukkan yan Igbo mazauna arewa da su bar yankin kafin ranar 1 ga watan Oktoba.

Yanzu Yanzu: Matasan arewa na cikin ganawa da Ndigbo dake Kano kan wa’adin barin gari

Yanzu Yanzu: Matasan arewa na cikin ganawa da Ndigbo dake Kano kan wa’adin barin gari

Taron na Kano na zuwa ne domin a tattauna don kawo karshen rigimar, bayan shugaban kungiyar AYCF, Shettima Yerima y adage cewa lallai suna nan akan bakar su.

KU KARANTA KUMA: Gwamnati na iya kokarin ceto ma’aikatan da aka sace - Osibanjo

Yarima ya bayyana cewa kungiyar zata ci gaba da tattaunawa da mutanen arewa maso tsakiya da kuma arewa maso gabas don jin makomar idan zasu sauya matsayarsu.

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Online view pixel