Gwamnatin Tarayya za ta gyara tituna a jihohin Plateau da Kwara

Gwamnatin Tarayya za ta gyara tituna a jihohin Plateau da Kwara

Ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ya sanar da cewa gwamnatin tarayya zata yi aiki a titunan jihar Plateau da ta jihar Kwara da kudi da yawansu ya kai kimanin naira biliyan 20.6

Fashola ya sanar da hakan ne ga manema labarai a lokacin da aka kammala zaman majalisa (FEC) wanda mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya shugabanta a ranar Laraba, 2 ga watan Yuli.

A cewarsa an yarda da kashe naira biliyan 10.4 gurin gyaran titin Pankshin-Balank-Yalen-Salak-Gindiri na jihar Plateau sannan kuma za’a yi amfani da naira biliyan 10.2 gurin gyaran titin Sharre-Patigi dake jihar Kwara.

Gwamnatin Tarayya za ta gyara tituna a jihohin Filato da Kwara

Gwamnatin Tarayya za ta gyara tituna a jihohin Filato da Kwara

KU KARANTA KUMA: Gwamnati na iya kokarin ceto ma’aikatan da aka sace - Osibanjo

Daga karshe Fashola ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gama zantawa da take yi da wani kamfani da zai samar da sababbin mitocin wutar lantarki guda miliyan uku.

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel