Bana da-na-sanin karya aniyar Obasanjo ta tazarce - Ken Nnamani

Bana da-na-sanin karya aniyar Obasanjo ta tazarce - Ken Nnamani

- A 2006 shugaban lokacin Obasanjo ya nemi ya zarce a zango na uku

- Majalisa ta rabu, anyi musu ruwan daloli buhu-buhu

- Nnamani ya koma APC, kuma ya waiwaya don tsokaci

Tsohon shugaban majalisar dattijai, Ken Nnamani, yace baya da-na-sanin karya aniyar shugaba Olusegun Obasanjo da yayi daga neman kara yin tazarce a karo na uku. Nnamani ya kara da cewa in yau ma za’a sake dawo da maganar, zai sake soke ta.

Bana da-na-sanin karya aniyar Obasanjo ta tazarce - Ken Nnamani
Bana da-na-sanin karya aniyar Obasanjo ta tazarce - Ken Nnamani

Yayi wannan magana ne a taron kasa mai taken “Hadin-kai da Tsaro a Kasa” da aka yi a ma’aikatar DSS, yankin koyan harkar tsaro a Abuja.

Nnmani ya kara da cewa ya kamata kuma a canja salon tsarin mulkin Najeriya.

“Ina so in yi magana a kan wannan batu. Kar ku dau maganar shugaban ’yan-sanda na kasa, wato Solomon Arase, da yace bin shugaban kasa sau-da-kafa ya wadatar da yiwa Najeriya biyayya. Hakan ba dole bane ya zama dai-dai.”

DUBA WANNAN: 'Yan kunar bakin-wake 2 sun kai hari babban asibitin Maiduguri

“Wadanda suke sukar maganar sabunta tsarin mulki a yanzu sai sun ga ribar shi in aka yi. Abin da wata jiha ke iyawa wata bata iyawa. Misali, abin da zaka shuka a Arewa ba dole bane ka shuka shi a Kudu ba kuma ya fito. Saboda haka kowa na bukatar juna. Masu maganar cewa wasu jihohin zaman kashe wando kawai suke yi ana basu kudi ba dai-dai bane. In muka hada kai, duk zamu ci gaba gaba daya a tare.”

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel