EFCC sai ta bayyana ma na binciken ta - Malami

EFCC sai ta bayyana ma na binciken ta - Malami

- Hukumar EFCC ta na gudanar da bincike ba tare da tuntubar cibiyar alkalanci ta kasa ba

- Shugaban alkalanci na kasa ya umarci hukumar EFCC da ta bayyanawa cibiyar alkalanci duk wasu binciken da za ta gudanar

Ministan Alkalanci kuma lauyan kolu na Najeriya, Abubakar Malami ya umarci hukumar bincike a kan laifukan kudi (Economic and Financial Crime Commission, EFCC) da ta bayyanawa cibiyar alkalanci duk wani bincike da za ta gudanar.

Lauyan ya ce wannan umarnin a kan hukumar da shugabanta, Ibrahim Magu ya yi daidai ne sharuddan da ka'idojin hukumar binciken na 2010.

Cibiyar Alkalanci ta yi wannan umarnin ne a wata wasika aikawa hukumar da lauya Abiodun Aikomo ya rubuta a madadin lauyan kolu.

EFCC sai ta bayyanar da binciken ta - Malami

EFCC sai ta bayyanar da binciken ta - Malami

Cibiyar Alkalancin ta na tuhumar hukumar EFCC da rashin bin ka'idoji da sharudda da ita hukumar ta gindaya a sashe na 10 cikin jerin sharuddan na ta kuma cibiyar ta na bukatar hukumar ta karkata akalar ta wajen bin wannan ka'idoji.

Lauya Abiodu ya rubuta a cikin wasikar kamar haka: "Ministan Alkalanci ta kasa baki daya kuma lauyan Kolu na Najeriya ya umarce ni na rubuta wannan wasika zuwa ga hukumar EFCC da na tunatar da ita sharuddai da ka'idojin ta da ta gindaya na 2010 kuma ta buga a cikin jaridar gwamnatin tarayya mai lamba 61 ta ranar 21 ga watan Satumba na 2010 musamman ma sharudda da ka'idojin da su ka wajaba a kan hukumar.

An umarce ni da na tunatar da hukumar sashen ta na 10 wanda ya ke nuna wajabcin hukumar da ta aikawa Lauyan kolu duk wani bincike da hukumar za ta gudanar a kan manyan laifuka, sakamokon binciken ta da kuma ta cewar ta a kan wannan bincike wanda za bayu ga nuna dalilai na cancantar gurfanar da wanda a ke bincika.

KU KARANTA: Yajin Aiki: Ma'aikatan kwalejin ilimi ta jihar Legas sun gyara zaman su

Lauyan Kolu na kasa ya lura da cewa hukumar ta EFCC ba ta bin wannan ka'ida da sharadi da ta gindaya wa kanta a wasu lokuta, saboda haka wannan wasika tunatarwa ce ga hukumar don ta nazari kuma ta bi sharudai da ka'idojin da su ka rataya a kan ta.

Ina rokon karbar wannan wasikar da hannu biyu-biyu kuma ina bayar da tabbacin na miko gaisuwa daga lauyan kolu."

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel