Kungiyar Boko Haram ta saki bidiyon ma’aikatan jami’ar Maidugurin da tayi garkuwa da su

Kungiyar Boko Haram ta saki bidiyon ma’aikatan jami’ar Maidugurin da tayi garkuwa da su

- Yan Boko Haram sunyi garkuwa da malaman jami'ar Maiduguri da jami'an NNPC

-Daga baya an gano wasu daga cikinsu amma a mace

An samu sabon tashin hankali bayan yan kungiyar Boko Haram ta hallaka masu hakan man fetur da malaman jami’ar Maiduguri, ta sake sakin wani bidiyon da ke nuna malaman jami’ar 3 da tayi garkuwa da su.

A bidiyon da tashar Channels ta samu, mazaje ukun da aka sunce su ma’aikatan jami’ar Maiduguri ne kuma suna neman taimakon gwamnatin tarayya.

Kungiyar Boko Haram ta saki bidiyon ma’aikatan jami’ar Maidugurin da tayi garkuwa da su
Kungiyar Boko Haram ta saki bidiyon ma’aikatan jami’ar Maidugurin da tayi garkuwa da su

Biyu daga cikinsu sunce su malaman sashen ilimin duwatsu na a jami’ar kuma sunayensu shine Yusuf Ibrahim da Dakta Solomon N. Yusuf. Na ukun mai suna Haruna direba ne a jami’ar.

KU KARANTA: Dangote ya bayyana sirrin arzikinsa

Sunce suna cikin tawagar masu hakan man da Boko Haram ta far mawa ranan Talata, 25 ga watan Yuli, 2017.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

Don bamu shawara ko labarai, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel