Kasuwa ta yi riba - Dangote ya dara

Kasuwa ta yi riba - Dangote ya dara

- Mai rabon ganin badi sai ya gani, don aljihun Dangote ya kusan fara zuba

- Kasuwancin Dangote ya yi kundubala ya harba sama

Shugaban gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya kara nusuwa cikin jerin masu kudin duniya yadda kudin shi a yanzu sun kai dalar amirka biliyan 16.2

A wata kididdiga da masu tantancewar nan ta duniya, FORBES, su ka yi a ranar Alhamis din da ta gabata sun bayyana cewa Aliko Dangote ya kara harbawa sama a cikin dukiya.

Kididdigar ta bayyana cewa Dangote ya samu kari ne akan kudin shi na da dalar Amirka miliyan 162 inda su ka koma zuwa dalar Amirka biliyan 16.2.

Kasuwa ta yi riba - Dangote ya dara

Kasuwa ta yi riba - Dangote ya dara

A wannan halin ne mai kamfanin layin sadarwa na GLO, Mike Adenuga ya samu ribar dalar Amirka miliyan 7 , wanda a yanzu ya na da dalar Amirka biliyan 6.2

KU KARANTA: Kunji yawan kudin da kanal Hamid Ali ya tarawa gwamnatin tarayya

Sai kuma shugaba kuma mai kamfanin Famfa Oil Limited, Mrs. Folorunsho Alakija wadda ita ta na nan ba ta yi sama ba kuma ita ba ta yi kasa ba da zunzurutun kudi dalar Amirka biliyan 1.2

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel