Shugaba Buhari ya ji sauki sannan kuma zai dawo Najeriya kwanan nan – Gwamna Ganduje

Shugaba Buhari ya ji sauki sannan kuma zai dawo Najeriya kwanan nan – Gwamna Ganduje

- Gwamna Ganduje ya ce shugaba Buhari na jin sauki sosai

- Ya ce shugaban kasar zai dawo kwanan nan

- Shi da wasu gwamnoni shidda suka kai ma shugaban kasar ziyara birnin Landan

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nuna farin cikin sa kan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu lafiya sosai jim kadan bayan shi da wasu gwamnoni shidda sun gana da shi.

Gwamnonin wadanda aka zaba domin su wakilci sasssa shidda na kasar sun samu jagorancin gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari wanda ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.

Sun gana da shugaban kasar a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, a birnin Landan inda ya share sama da kwanaki 60 yana jinya.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumin kirista ya musulunta a Borno, ya chanja suna zuwa Abubakar

Bayan ganawar Ganduje ya ce:

“Daga abubuwan da muke ji, mun ga cewa shugaban kasar ya ji sauki sosai. Mun ji dadin ganinsa. Ya fito da kansa don ya yi musabaha da mu sannan ya koma ya zauna. Shugaban gwamnoni ya bayar da takaitaccen jawabi sannan shi (shugaba Buhari) ya maida martani sannan yay i barkwanci.

“Don haka nayi imani da cewa shugaban kasa zai ji sauki gaba daya kwanan nan sannan ya dawo Najeriya.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

Don bamu shawara ku aiko mana da labarai, tuntubemu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel