Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Rahotanni sun kawo cewatawagar masu gangami ba su samu damar ganawa da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ba, saboda gwamnatinsa ta hana kaddamar da gangami.

Tawagar wasu mata ne suka gudanar da zanga-zanga bisa yadda alummar jihar Kano suka yi watsi da gagarumar matsalar da ta addabi jihar ta yawan fyade.

Wata mata daga cikin masu zanga-zangar da aka ambata da suna Hajiya Aisha Dan kani ta bayyana cewa sun gudanar da zanga-zangar ne dmin tunasar da alúmma kan hakkin day a rataya a wuyansu na kawo karshen matsalar yawan fyade.

Tsoffin daliban makarantar St. Louis ne suka shirya gangami sai dai gwamnatin jihar Kano ta hana kaddamar da zanga-zangar, ta ci gaba da gudana duk da cewan basu samu damar ganawa da gwamnan jihar ba kamar yadda aka tsara.

Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Likitoci sun tabbatar da cewa aikata fyade na karuwa a jihar Kano maimakon ace ya ragu, harma wata kididdiga ta nuna cewa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017, an samu rahoto na aikata fyade fiye da 700 a jihar, kuma kashi 45 cikin 100 na wadanda aka yi wa fyaden kananan yara ne masu karancin shekaru.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo zai rantsar da sababbin ministoci gobeOsinbajo zai rantsar da sababbin ministoci gobe

Matan sun jure duk da rowan sama da aka ta sheka a lokacin zanga-zangar a safiyar ranar Talata, 25 ga watan Yuli, sannan sun kasance dauke rubuce-rubucen da suka hadarda “kada a yi fyade” da kuma “a rika hukunta masu fyade”.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

Don bamu shawara ku aiko mana da labarai, tuntubemu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel