Hukumomin kare hakkokin bil adama sun kai karar Ishaku ICC sakamakon kashe-kashen da ya auku a Taraba

Hukumomin kare hakkokin bil adama sun kai karar Ishaku ICC sakamakon kashe-kashen da ya auku a Taraba

Hukumomin sun nemi kotun duniya mai lura da ta'ardanci (The International Criminal Court, ICC) da tayi bincike gameda yawan kashe-kashen da yake aukuwa a jihar ta taraba.

A koke-koken da kungiyoyin da suka kai kotun Legit.ng ta ruwaito cewa sun rubutawa ofishin Madame Fatou Bensouda ire-iren abubuwan dake aukuwa a jihar na kisa da sauran jihohin kasar baki daya.

kararrakin da korafe-korafen dai sun fito ne daga kungiyar; civil society organization da kungiyar Save Humanity Advocacy Centre ta hannun babbandu Alexandra Thome.

Hukumomin kare hakkokin bil adama sun kai karar Ishaku ICC sakamakon kashe-kashen da ya auku a Taraba
Hukumomin kare hakkokin bil adama sun kai karar Ishaku ICC sakamakon kashe-kashen da ya auku a Taraba

kari akan gwamnan da kungiyoyin ke tuhuma akwai kuma dan majalisar jihar Abel Diah da ciyaman na karamar hukumar Sardauna, John Yep.

korafe-korafen sun biyo bayan rikicin da ya auku a jihar na 17 ga watan Yunin shekarar 2017 tsakanin mazauna Nguroje da masu kiwon shanun Mambilla daga karamar hukumar Sardauna a Jihar ta Taraba.

A jawaban nasu hasararorin da akayi Legit.ng ta ruwaito cewa an kashe shanaye 17,000, an kona gidaje,tareda kashe mutane a bangarori da dama na yankunan.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya yamutsa majalisar gudanarwar sa

Kungiyoyin sun nuna cewa akwai yiwuwar zanga-zanga da wasu mazaunan yankin zasuyi don nuna rashin jin dadin abubuwan dake faruwa sakamakon kin daukan mataki da gwamnan Jihar yayi.

A bayada cin hanci da rashawa da kasar Najeriya ke fama dashi, akwai rashin bada kulawa ga hakkokin bil Adama da hukumomin kasar keyi.

wannan shine dalilan da sukasa kungiyoyin suka kai karar ga babbar kotun ta ICC ta duniya domin kawo dauki da magance abubuwan dake aukuwa a Jihar.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel