Hukumar sojojin Najeriya ta ragewa wani Manjo Janar matsayi sakamakon Rashawa da yayi

Hukumar sojojin Najeriya ta ragewa wani Manjo Janar matsayi sakamakon Rashawa da yayi

- Kotun sojojin ta nemi Manjo janarda din ya dawo da kudade naira miliyan N23 da ya karba a sayarda wasu filayen hukumar da yayi

Wata babbar kotun soja a ranar Lahadi ta ragewa Manjo Janar Ibrahim Sani da wani shugaban kirkire-kirkiren hukumar matsayi, zuwa ga matakin Birgediya janar.

Shugaban kotun,Air Vice Marshal James Gbum, ya ragewa Sani matsayin ne bayan kamasa da laifuruka biyar dakeda alaka da cin hanci da rashawa.

Hukumar sojojin Najeriya ta ragewa wani Manjo Janar matsayi sakamakon Rashawa da yayi
Hukumar sojojin Najeriya ta ragewa wani Manjo Janar matsayi sakamakon Rashawa da yayi

Mr. Sani ya kasance yana fuskantar hukunci daga kotun tun daga shekarar 2015 bayan kamasa da raba wani yanki na kasar hukumar sojoji wa kansa.

Kotun dake zaune a Mogadishu Cantonment, Asokoro, Abuja,ta sake neman Mr. Sani da ya dawo da kudade naira miliyan N23 da ya karba a sayarda wasu filayen hukumar da yayi.

kotun ta bada sanarwa inji Legit.ng cewa ya mallakawa kansa filin kasa da ya kai heka 436

(hectares) a yayinda ya sayar da wani bangaren wa wasu.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya yamutsa majalisar gudanarwar sa

Shugaban kotun ya bayyana cewa Mr. Sani ya kai matuka gun wuce iyaka a sabawa dokar hukumar sojoji ta hanyar amfani da takardun mallaka na bogi tareda sanya hannun karya gun sayar da filayen wa wadanya ya sayarwa.

Mr. Gbum ya nuna cewa sojan ya sayar da filayen wa mutane daban daban har uku akan kudade miliyan N10 million, N7 million da N6 million, respectively.

A karshe aAlkalin ya nuna cewa zartarwar kotun da hukuncin da tayi masa ya kasance ne bisa tsarin kundin hukumar ta soja.

Mai bada shawara wa Mr sani, Paul Suleya nuna cewa zai daukaka karar a kotun daukaka kara don waiwayen hukuncin, idan kuma bai yiwu ba zai kai ga babbar kotu.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel