Gwamnatin kano ta jibinci nauyin tirenin din yan kwallon Eagles don tarar wasan CHAN

Gwamnatin kano ta jibinci nauyin tirenin din yan kwallon Eagles don tarar wasan CHAN

- Horon yan kwallon zai fara daga ranar Litinin 24 ga watan Yuli, shekarar 2017

Gwamnatin Jihar Kano ta karbi jibintar nauyin kintsin da 'yan wasan najeriya shuper eagles zasuyi a Jihar don shiryawa tarar wasan kwallon kafa na Afurka (African Nations Championship CHAN). Ana tsammanin wasan zai kasancene tsakanin Najeriya da KasarBenin ko Togo.

Wannan jawaban sun fito ne daga bakin Babban sakataren kungiyar wasan kwallon kafan Najeriya (Nigeria Football Federation NFF), Dr. Mohammed Sanusi.

Gwamnatin kano ta jibinci nauyin tirenin din yan kwallon Eagles don tarar wasan CHAN
Gwamnatin kano ta jibinci nauyin tirenin din yan kwallon Eagles don tarar wasan CHAN

Sanusi ya bayyanawa NFF ta shafinsu na yanar gizogizo a cewar Legit.ng irin yarda da murnar tarbar bakin da zasuyi wanda kungiyar ta nema, kuma zai fara daga ranar Litinin 24 ga watan Yuli, shekarar 2017.

Tawagar ta Super Eagles zasu bar Jihar ta kano a 11 ga watan Agusta don fuskantar abokan dagansu a wasan zuwa CHAN din, kuma zasu dawo kasar a jihar kano a 19 ga watan Agusta don karon wasan na biyu.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya yamutsa majalisar gudanarwar sa

Kasar togo da Benin sun doka wasan kunnen doki mai sakamako 1-1 a karon farkon wasan nasu,a Lome satin da ya gabata, karo na biyu kuma zai kasance ne a kwatano a ranar Lahadi mai zuwa.

Duk wanda yayi nasara a cikinsu ne zai fuskanci yan wasan na Super Eagles a filin wasan kwallon Sani Abacha dake kano.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel